DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Kayan aikin dake filin jirgin saman Legas tsofaffi ne, akwai buƙatar yin gyara cikin gaggawa – Ganduje

-

 

Ganduje

Google search engine

Shugaban hukumar gudanarwa ta hukumar kula da filayen jiragen sama ta Nijeriya FAAN, Dr. Abdullahi Ganduje, ya jaddada bukatar gyara filin jirgin saman Legas na Murtala Muhammed cikin gaggawa saboda kayan aikin da ke filin jirgin saman sun tsufa.

Yayin ziyara ta farko da ya kai tare da rakiyar babbar daraktar hukumar ta FAAN, Olubunmi Kuku, Ganduje ya tabbatar da cewa yawancin kayan aikin filin jirgin sun lalace.

Ganduje ya kuma bayar da tabbacin cewa hukumar za ta hada kai da hukumomi domin inganta filayen jirgin sama ta yadda za su yi gogayya da na duniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Tsare-tsaren Tinubu na farfaɗo da martabar Nijeriya a duniya -Kashim Shatima

Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya ce gyare-gyaren da gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na sake gina martabar Nijeriya a idon duniya tare...

Gwamnatin Nijeriya na shirin dakatar da shigo da kayan tsaro daga waje

Gwamnatin Nijeriya ta yi niyyar kera dukkan makami da ake buƙata a cikin gida nan da shekara biyu zuwa biyar masu zuwa. Minista a ma'aikatar Tsaron...

Mafi Shahara