DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jirgin Sojin saman Nijeriya ya halaka ‘yan bindiga,da dama tare da kwato Shanu da suka sace

-

 

Dakarun sojojin saman Nijeriya karkashin Operation Fansar Yamma sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da dama a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda suka kwato wasu shanu da dama da aka sace.

Wata majiya ta shaida wa kwararre kan harkokin yada labarai na yaki da ‘yan ta’adda Zagazola Makama, cewa an samu nasarar gudanar da wannan aiki ne ta hanyar samun bayanan sirri, da ya nuna cewa wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan uwan ​​fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne, Ado Aleiro, tare da wasu mutanen da ba a san ko su waye ba,a Tsafe ta jihar Zamfara suna satar shanu daga al’ummomin da ke kusa.

Majiyar ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace dabbobi da dama kuma suna yunkurin tserewa ne a lokacin da suka fuskanci turjiya daga jami’an tsaron yankin.

Sojojin sun bi sawun barayin kuma sun jira har sai da suka isa wani wuri mai tsaunuka kafin su kewaye su.

Bayan tabbatar da inda suke, sai suka sanar da rundunar sojojin saman Nijeriya, da ta yi gaggawar tura jirage na sama domin tunkarar ‘yan bindigar da suka tsere.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an kawar da ‘yan bindigar da dama a yayin harin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin su ba. Wata majiya ta biyu ta ce an kashe akalla ‘yan bindiga 23, yayin da wasu da dama suka jikkata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Kwamishinan Jigawa ya mayar da rarar Naira miliyan 301 daga kudaden da aka ware don shirin ciyar da al’umma a watan Ramadan

Kwamishinan ayyuka na musamman na jihar Jigawa, Alhaji Auwalu Danladi Sankara, ya mayar da Naira miliyan 301 zuwa baitul malin jihar, daga cikin Naira biliyan...

Gwamnatin mulkin sojin Nijar ta karɓi wasikun kulla kawance daga sabbin jakadun ƙasashe 8

A ranar Juma’a, 9 ga Mayu, 2025, fadar gwamatin ta Jamhuriyar Nijar ta karɓi sabbin jakadun daga jakadun ƙasashen duniya guda takwas. Inda shugaban mulkin sojin...

Mafi Shahara