DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Jirgin Sojin saman Nijeriya ya halaka ‘yan bindiga,da dama tare da kwato Shanu da suka sace

-

 

Dakarun sojojin saman Nijeriya karkashin Operation Fansar Yamma sun yi nasarar fatattakar ‘yan bindiga da dama a karamar hukumar Tsafe ta jihar Zamfara, inda suka kwato wasu shanu da dama da aka sace.

Wata majiya ta shaida wa kwararre kan harkokin yada labarai na yaki da ‘yan ta’adda Zagazola Makama, cewa an samu nasarar gudanar da wannan aiki ne ta hanyar samun bayanan sirri, da ya nuna cewa wasu gungun ‘yan bindiga da ake zargin ‘yan uwan ​​fitaccen shugaban ‘yan bindiga ne, Ado Aleiro, tare da wasu mutanen da ba a san ko su waye ba,a Tsafe ta jihar Zamfara suna satar shanu daga al’ummomin da ke kusa.

Majiyar ta bayyana cewa ‘yan bindigar sun sace dabbobi da dama kuma suna yunkurin tserewa ne a lokacin da suka fuskanci turjiya daga jami’an tsaron yankin.

Sojojin sun bi sawun barayin kuma sun jira har sai da suka isa wani wuri mai tsaunuka kafin su kewaye su.

Bayan tabbatar da inda suke, sai suka sanar da rundunar sojojin saman Nijeriya, da ta yi gaggawar tura jirage na sama domin tunkarar ‘yan bindigar da suka tsere.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa an kawar da ‘yan bindigar da dama a yayin harin, duk da cewa har yanzu ba a tantance adadin su ba. Wata majiya ta biyu ta ce an kashe akalla ‘yan bindiga 23, yayin da wasu da dama suka jikkata.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 kudin ritayarsu

Gwamna Abba K. Yusuf ya amince a biya kudin fanshon fiye da Naira biliyan 15 ga tsofaffin Kansilolin gwamnatin Ganduje sama da 3000 Wadanda abin ya...

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da ‘ya’yanta ke yi

PDP za ta tattauna da gwamnoninta kan sauya shekar da 'ya'yanta ke yi nan da makon gobe Kwamitin gudanarwa na kasa (NWC) na jam’iyyar PDP tare da kungiyar gwamnonin...

Mafi Shahara