DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Mune ‘ya’yan jam’iyyar NNPP ta asali, Alhassan Rurum yayi fatali da dakatarwar da jam’iyyar NNPP ta yi masu a Kano

-

Dan majalisa mai wakiltar mazabar Rano, Kibiya, da Bunkure a majalisar wakilan Nijeriya, Hon. Kabiru Alhassan Rurum, ya yi watsi da dakatarwar da aka yi masa daga jam’iyyar NNPP a Jihar Kano.

Google search engine

Da yake mayar da martani kan sanarwar dakatarwar da shugaban jam’iyyar NNPP na jihar Kano, Hashim Sulaiman Dungurawa ya fitar, Kabiru Alhassan Rurum ya ce shi da takwarorinsa da aka dakatar ba su taba bin bangaren da suka sauya tambarin jam’iyyar ba, yana mai jaddada cewa suna cikin jam’iyyar ta asali.

A baya dai Alhassan Rurum da Aliyu Sani Madakin Gini sun fito fili sun ware kansu daga tafiyar Kwankwasiyya tare da jaddada kansu a cikin Jam’iyyar NNPP mai alamar kayan marmari.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Shugaba Tinubu adali ne, bai fifita kowane yanki ba wajen rarraba ayyukan ci-gaba ba a Nijeriya – Gwamnatin tarayya

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana cewa shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu na gudanar da mulkinsa bisa gaskiya da adalci wajen rabon ayyuka, mukamai da damar ci-gaba...

Dalilin da ya sa muka maye gurbin rundunar Operation Safe Haven da Enduring Peace – Babban hafsan tsaron Nijeriya

Babban hafsan tsaron Nijeriya, Janar Christopher Musa, ya ƙaddamar da sabuwar rundunar haɗin gwiwa mai suna Operation Enduring Peace domin magance matsalar tsaro da ta...

Mafi Shahara