DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An caccaki Ganduje kan kokarin APC na lashe zabe a jihar Kano

-

 

Abdullahi Umar Ganduje

Shugaban jam’iyyar NNPP reshen jihar Osun, Tosin Odeyemi, ya caccaki shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Ganduje, kan shirin jam’iyyarsa na karbe Kano a zaben gwamna mai na 2027.

Google search engine

Tosin Odeyemi ya ce babu yadda za ai APC ta lashe zaben kano domin talakawan jihar basa tare da su,suna goyon bayan Abba Kabir Yusuf.

Da yake mayar da martani ga shugaban jam’iyyar APC na kasa, wanda ya bayyana NNPP a matsayin matacciyar jam’iyyar a Kano, Odeyemi, a wata sanarwa da ya fitar, ya ce ya zama wajibi Ganduje ya farka daga dogon mafarkin da yake yi na karbar mulki a jihar.

Sanarwar ta kara da cewa babu yadda za ai al’ummar kano suyi kuskuren zaben jam’iyyar APC a nan gaba domin jihar kano na hannun NNPP.

Ya ce abin mamaki kaji wanda ke zaune a wani wuri mai nisa da jiharsa ta ya yi takamar mutane da yawa daga cikin NNPP sun shirya ficewa daga jam’iyyar zuwa APC.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

NAHCON ta gargadi maniyyata Hajjin 2026 na Nijeriya kan yin rijista da wuri

By Fatima Aminu Dabo Hukumar jin daɗin alhazai ta kasa NAHCON ta sanar da jadawalin aikin Hajjin 2026, inda ta bayyana cewa 20 ga Maris, 2026...

Ana ci gaba da neman wata dattijuwa bayan kifewar kwale-kwale dauke da fasinja 11 a Sokoto

An gano gawar wani matashi mai shekara 29 da ya rasa ransa a wani hatsarin jirgin ruwa da ya afku a Jihar Sokoto.Lamarin ya faru...

Mafi Shahara