DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar NDLEA ta lalata tan 25 na miyagun kwayoyi a Kogi

-

NDLEA 

Hukumar hana da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Nijeriya NDLEA reshen jihar Kogi ta lalata tan 25 na miyagun kwayoyi a Lokoja babban birnin jihar a ranar Laraba.

Google search engine

Wakilin shugaban hukumar NDLEA Brig. Janar Mohammed Buba Marwa a wajen taron, daraktan ayyuka da bincike na hukumar ta NDLEA, Ahmed Suleiman Ningi, ya jaddada illar da ke tattare da irin wadannan haramtattun magunguna.

Ya ce idan aka bari mutane na amfani da haramtattun magunguna irin haka,yana iya kara tsananta kalubalen tsaro a cikin kasar.

Kwayoyin da aka lalata sun hada da, Tramadol, Rohypnol, Diazepam, Exol-5, Pentazocine da  Cocaine.

Kwamandan hukumar NDLEA na jihar Kogi, Umah Mustapha Yahuza, ya bayyana cewa an kama motoci 24 na masu safarar miyagun kwayoyi tare da kwacesu. 

Ya bukaci hadin kan al’umma wajen yaki da fataucin miyagun kwayoyi, ya kuma bayyana cewa akwai karin tan biyar na haramtattun kwayoyi har yanzu ana ci gaba da shari’a akai.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaba Tinubu ta soki Atiku kan kwatanta gwamnatinsa da ta mulkin soja

Fadar Shugaban Nijeriya ta caccaki madugun adawa Atiku Abubakar, bisa kwatanta gwamnatin Tinubu da mulkin soja, tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin abinda basu...

Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan gyaran dokar zabe tare da shiga zaman sirri

Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar da muhawarar kan kudirin dokar zaɓe ta 2022, domin bai wa ’yan majalisa damar yin nazari mai zurfi kafin ɗaukar...

Mafi Shahara