An bindige shugaban kungiyar Miyetti Allah na jihar Kwara

-

 

‘Yan bindiga sun bingige shugaban kungiyar Miyetti Allah reshen jihar Kwara, Alhaji Idris Abubakar Sakaina.

Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin karfe 10:00 na daren ranar Asabar, da maharan suka harbe shi har lahira a kofar gidansa da ke Oke Ose a birnin Ilorin.

A cewar Jaridar Daily Trust ‘yan bindigar sun bar shi a nan cikin jini ba tare da sun dauki wani abu nasa ba.

Marigayin mai shekaru 32, an ce tsohon mataimaki na musamman ne ga shugaban karamar hukumar Moro kuma shugaban matasan Fulanin jihar Kwara.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Mun ji takaicin ficewar gwamna Sheriff Oborevwori na jihar Delta daga PDP zuwa APC- Umar Damagum

Shugaban ruko na jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana ficewar Gwamna Sheriff Oborevwori na Jihar Delta, tare da wasu manyan jiga-jigan jam’iyyar zuwa...

Talauci zai karu a Najeriya nan da 2027 – Bankin Duniya

Bankin Duniya ya bayyana cewa yawan mutanen Najeriya da ke fama da talauci zai karu nan da shekarar 2027, duk da kasancewar kasar na daga...

Mafi Shahara