DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Cire tallafin man fetur munyi shi ne da kyakyawar manufar kare makomar matasan Nijeriya – Shugaba Tinubu

-

Shugaba Bola Ahmad Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya ce duk wani mataki da ya dauka har zuwa yanzu, ciki har da batun cire tallafin man fetur ya shafi matasan Nijeriya ne da kuma makomar su.

Google search engine

Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin kaddamar da kwamitin tsare-tsare na taron matasa na kasa a fadar gwamnati da ke Abuja.

Ya ba da tabbacin cewa, an yi gyare-gyaren tattalin arzikin ne domin karfafa tattalin arzikin kasar don samar da wadata ga matasan Nijeriya, wadanda su ne sama da kashi 60 cikin dari na al’ummar kasar.

Ya tabbatar da cewa matasa sune fatan Nijeriya, kuma komai ya rataya a kan su, da ya ce duk shawarar da ya yanke saboda matasan ne ciki harda cire tallafin man fetur don kare makomar su.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

‘Yan majalisar dokoki 6 a Jihar Zamfara sun fice daga PDP zuwa APC

‘Yan Majalisar Dokokin Jihar Zamfara 6 da aka zaɓa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP sun sauya sheƙa zuwa jam’iyya mai mulki ta APC, suna zargin take...

Kotu ta umurci hukumar EFCC ta gabatar da kwamshinan kudi na jihar Bauchi ga kotu bisa zargin safarar N4.6bn

Kotun Tarayya da ke Abuja ta umurci Hukumar EFCC da ta gabatar da Kwamishinan Kuɗin Jihar Bauchi, Yakubu Adamu, a ranar 30 ga Disamba domin...

Mafi Shahara