![]() |
Malam Nasir El-Rufa’i |
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ya musanta zargin cin amanar tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar jam’iyyar PDP Atiku Abubakar.
Da yake magana a wata hira da BBC Hausa,El-Rufai wanda ya fice daga jam’iyyar APC zuwa SDP,cikin makon da ya gabata, ya bukaci shugabannin adawa da suka hada da Atiku Abubakar, Peter Obi na Labour Party, tsohon gwamnan jihar Ribas, Rotimi Amaechi, da Rauf Aregbesola, da su koma jam’iyyar SDP.
Da yake bayyana rashin jin dadinsa da gwamnati mai ci, El-Rufai, ya bayyana takaicinsa bisa yadda suka goyi bayan shugaba Tinubu da nufin kawo ci gaba domin sunga yadda ya kai wa Legas ci gaba.