![]() |
Tunji Alausa |
Ministan Ilimi Tunji Alausa, ya bukaci majalisar dokokin Nijeriya ta dakatar da aiki kan kudirin kafa sabbin jami’o’i
Da yake jawabi a wajen taron manema lanarai na ministoci da aka yi a Abuja, Tunji Alausa ya koka da yadda jami’o’i ke kara yawa yayin da wadanda ake da su ke fama da kalubalen kudade.
Ministan ya yi kira ga ‘yan majalisar tarayyar, da su dakatar da kudurin kafa sabbin jami’oin domin suna cin kudade da yawa, inda ya ce zuwa yanzu akwai kudirori kusan 200 a gaban majalisar dokokin kasar na kirkiro sabbin jami’o’i, kuma wadanda ake da su babu isassun kayan aikin tafiyar da su.
Don haka ya bukaci maimakon kafa sabbin makarantu, kamata ya yi a inganta wadanda ake da su.