Rundunar sojin saman Nijeriya ta bayyana cewa, wasu hare-hare ta sama da jami’an tsaro suka kai a jihar Katsina sun lalata maboyar ‘yan ta’adda a dajin Unguwar Goga da ke unguwar Ruwan Godiya a karamar hukumar Faskari ta jihar.
Rundunar sojin karkashin Operation Fansar Yamma ta kai harinne da sanyin safiyar ranar Alhamis, a sansanonin ‘yan bindiga guda biyu, Gero Alhaji da kuma Alhaji Riga.
A wata sanarwa da mataimakin daraktan yada labarai da hulda da jama’a na rundunar sojin saman Nijeriya, Kaftin Kabiru Ali ya fitar a daren Juma’a, ta ce harin da jiragen suka kai sun yi nasarar halaka ‘yan bindiga sama da 20, tare da samun gagarumar nasara a kansu.