DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnonin Nijeriya sun yi kamun kafa ga Shugaba Tinubu da ya dakatar da tura kudin kananan hukumomi kai tsaye – Jaridar Punch

-

Gwamnonin jihohin Nijeriya sun fara wani yunkuri na dakatar da shirin tura wa kananan hukumomin kasar kason kudaden su kai tsaye, a daidai lokacin da ake ci gaba da samun tsaiko wajen aiwatar da hukuncin kotun koli kan ‘yancin cin gashin kai na ƙananan hukumomi.
Wasu daga cikin gwamnonin da suka gana da shugaban kasa Bola Tinubu a ranar Talatar makon jiya, sun yi watsi da matakin babban bankin Nijeriya CBN na tura kudin kai tsaye, inda suka bayyana cewa ana bin kananan hukumomin tulin bashi.
Majiyoyin jaridar Punch a fadar shugaban kasa sun ce, gwamnonin sun nemi shugaban da ya sake duba kan lamarin.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Obasanjo ya nuna jarumtaka da sadaukarwa wajen yi wa Nijeriya hidima – Shugaba Tinubu

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu, ya taya tsohon shugaban ƙasar Olusegun Obasanjo murnar cika shekaru 89 da haihuwa. A cikin wata sanarwa da mai magana da...

China ta umurci matatun man fetur din ta su dakatar da jigilar sa saboda rikicin Gabas ta tsakiya

Gwamnatin China ta umurci manyan matatun man fetur na ƙasar da su dakatar da fitar da dizal da fetur zuwa ƙasashen waje na ɗan lokaci,...

Mafi Shahara