![]() |
Zauren matasan Arewacin Nijeriya |
Zauren matasan Arewacin Nijeriya NYCN ya yi watsi da kudurin da aka gabatar na kara sabbin kananan hukumomi 37 a jihar Legas.
Shugaban zauren NYCN na kasa, Isah Abubakar, ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, inda ya bayyana kudurin da aka gabatar a matsayin rashin adalci da kuma barazana ga hadin kan kasa.
A Larabar da ta gabata ne dai majalisar wakilan Nijeriya ta yi karatu na biyu kan kudurin da ke neman karin ƙananan hukumomin daga 20 zuwa 57, wanda hakan ke nuna cewa adadin kananan hukumomin kasar zai karu daga 774 zuwa 811.