![]() |
Uba Sani |
Al’ummar Kauru da ke Kudancin Kaduna sun koka da yadda ‘yan ta’adda ke yin garkuwa da mutanen yankin tare da hallaka su ko da kuwa an biya su kudin fansa.
Kungiyar ci gaban al’ummar karamar hukumar Kauru ta nuna bakin ciki da bacin rai game da harin da aka kai wa al’ummar Surubu a masarautar Kumana, inda aka halaka mutane 3 duk da an biya kudin fansa, don haka suka roki gwamnati da ta samar musu da tsaro mai inganci.
A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun kungiyar, Duniya Achi, ya fitar, ta ce wannan danyen aikin na nuni ne da yadda matsalar tsaro ke kara kamari a karamar hukumarsu.