Kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar sun sanar da sabon harajin kashi 0.5 cikin 100 kan kayayyakin da ake shigowa da su daga Nijeriya da sauran kasashe mambobin kungiyar ECOWAS.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da kasashen da sojoji ke mulkinsu, ke kokarin samar da kudade ga sabuwar kungiyar kasashe uku bayan ficewa daga cikin ECOWAS.
A cewar wata sanarwa da kasashen suka fitar, an amince da harajin ne a ranar Juma’a kuma zai fara aiki nan take, kamar yadda gidan talabijin na Channels ya ruwaito.