Kwamandan birged ta daya na rundunar sojij Nalijeriya, Birgediya Janar Timothy Opurum, ya bayyana cewa sojojin dake karkashin Operation Fansar Yamma sun ci karfin ayyukan ‘yan ta’adda a yankin jihohin Kebbi da Zamfara.
Janar Opurum ya bayyana haka ne jiya Talata a yayin liyafar Sallah tare da hafsoshi, sojoji, da iyalansu a Gusau.
A cewarsa, lamarin tsaro a baya yana fuskantar kalubale, amma bisa ayyuka da sadaukar da kai da sojoji ke yi, sun samu galaba a yankin tare da dakile ayyukan ta’addanci da yawa.


