DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Rundunar ‘yan sandan Kano za ta yi bincike kan zargin take dokar hana yin hawan sallah a jihar

-

Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kafa kwamitin da zai bincike kan hatsaniyar da ta faru yayin da Sarki Muhammad Sanusi ke wucewa bayan gabatar da Sallar Idi, da kuma duk wani zargin take dokar hana yin hawan sallah da aka kafa a jihar.
Sanarwar da kakakin rundunar SP Abdullahi Haruna Kiyawa ya fitar tace, an É—ora wa kwamitin mai mutum takwas alhakin gano musabbabin faruwar tashin hankalin da ya yi sanadin rayuwar wani É—an vigilante É—aya da jikkata wani mutum É—aya.
Sanarwar ta kara da cewa, Kwamishinan ‘yan sandan Kano ya umurci kwamitin ya bincike zargin taka dokar hana hawan sallah da aka yi kuma tuni aka gayyaci Shamakin Kano, Alhaji Wada Isyaku domin amsa tambayoyi.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Hukumar zabe za ta hada kai da majalisar wakilan Nijeriya domin gudanar da sahihin zabe

Shugaban hukumar zaben Nijeriya INEC, Farfesa Joash Ojo Amupitan, ya bayyana aniyarsa ta yin aiki tare da Majalisar Dokoki domin tabbatar da gudanar da sahihin...

Jam’iyyar APC ta kalubalanci Gwamnan Filato Mutfwang da ya bayyana masu matsa masa lamba ya bar PDP

Jam’iyyar APC ta jihar Filato ta kalubalanci Gwamna Caleb Mutfwang da ya fito fili ya bayyana sunayen mutanen da ke matsa masa lamba ya bar...

Mafi Shahara