Dala biliyan 94.23, kwatankwacin naira tiriliyan N144.67, ne jimlar bashin da ake bin Najeriya a karshen shekarar 2024 da ta gabata, an samu karuwar kashi 48.58 cikin 100 kenan idan aka kwatanta da shekarar 2023, da ake bin Nijeriya bashin naira tiriliyan N97.34tn kwatankwacin dala biliyan $108.23, cewar rahoton ofishin kula da basussuka na kasar.
Sabon binciken da jaridar Punch ta wallafa ya nuna cewa an samu karuwar cin bashi daga kasashen waje da kuma cikin gida.
Binciken jaridar ya gano cewa bashin da ake bin Najeriya ya karu da naira tiriliyan N47.32tn, wanda ya nuna karuwar kashi 48.58 cikin 100 daga Disamba 2023 zuwa Disamba 2024.
Binciken ya kara da cewa, ya zuwa watan Disambar 2024, bashin kasashen waje ya kai kashi 48.59 cikin 100 na jimillar bashin da ake bin Najeriya, yayin da bashin cikin gida ya kai kashi 51.41 cikin 100.
Bashin da Nijeriya ta ciyo daga waje ya karu da kashi 83.89 wato dai daga naira 38.22tn a watan Disamba 2023 zuwa naira tiriliyan 70.29tn a watan Disamba 2024.
Gwamnatin tarayya ce ke da bashin Naira tiriliyan 62.92, yayin da jihohi da kuma babban birnin tarayya suke da bashin Naira tiriliyan 7.37 daga kasashen waje.
Hakama bashin cikin gida na Nijeriya ya karu da kashi 25.77 daga Naira tiriliyan 59.12tn a karshen watan Disamba 2023 zuwa Naira tiriliyan 74.38tn a watan Disamba 2024. Inda gwamnatin tarayya ce ke da bashin naira triliyan 70.41, sai kuma jihohi da babban birnin tarayya ke da bashin naira tiriliyan 3.97.
A cewar rahoton na ofishin kula da basussuka na Nijeriya, karuwar bashin bai rasa nasaba da sabbin rancen da ake samu daga waje da cikin gida da kuma faduwar darajar Naira.