Ministan Ilimin Nijeriya Olatunji Alausa, ya yi bukaci a tsawaita shirin yi wa kasa hidima daga shekara daya zuwa biyu.
Alausa ya bayyana haka ne a ranar Juma’a, lokacin da darakta janar na NYSC Birgediya Janar Olakunle Nafiu, ya kai masa ziyarar ban girma a ofishinsa da ke Abuja.
A cewar wata sanarwa da aka wallafa a shafin Facebook na NYSC, ministan ya kuma yi kira da a fadada shirin koyar da sana’o’i ga matasa a lokacin da suke hidimar kasar.