Dakarun runduna ta 6 Operation Whirl Stroke ta sojojin Nijeriya sun yi nasarar hallaka ‘yan bindiga uku, tare da lalata sansanonin ‘yan ta’addar da dama, da kuma kwato makamai da alburusai, a wani samame da suka kai a karamar hukumar Karim Lamido a jihar Taraba.
Farmakin ya gudana a ranar 5 ga Afrilu, 2025, a ci gaba da gudanar da ayyukan rundunar sojin na Operation Lafiya Jamaa wanda ke da manufar fatattakar ‘yan ta’adda daga jihar Taraba.
Wannan dai na kunshe a cikin wata sanarwar da mukaddashin mataimakin daraktan hulda da jama’a na rundunar soji ta 6, Captain Olubodunde Oni ya fitar.