Fadar shugaban kasa ta mayar da martani kan umarnin da hukumomin kasar Amurka suka bayar na fitar da bayanan sirri da aka samu kan shugaba Bola Tinubu.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito yadda wata kotun Amurka ta umarci hukumar FBI da ta fitar da bayanan kan binciken da aka yi wa Shugaban na Nijeriya.
Da yake mayar da martani, mai magana da yawun shugaban Bayo Onanuga, ya ce bayanan da ke cikin rahoton Agent Moss na hukumar FBI da kuma rahoton DEA, ba su tuhumi shugaba Bola Tinubu ba kuma rahoton ya shafe sama da shekaru 30 a bainar jama’a