![]() |
Jami’an hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi, NDLEA, sun kama wani mai shekaru 41 da haihuwa, kuma dan kasar Malaysia da ya dawo gida, Ndubuisi Udatu tare da wasu manya-manyan Sifiku guda biyu da aka yi amfani da su wajen boye wasu manya manyan kwayoyi mai nauyin kilogiram 2,700 domin rarrabawa a Yola da Mubi, da ke kan iyakar Kamaru da jihar Adamawa.
SolaceBase ta ruwaito cewa an kama Ndubuisi a cikin motar haya a wani shingen bincike na NDLEA a Namtari kan titin Ngurore-Yola, Adamawa, a ranar Litinin, 7 ga Afrilu, 2025.
An same shi da sabbin sifiku guda biyu da aka yi amfani da su wajen boye fakiti miyagun kwayoyin.