Shugaban mulkin sojin kasar Gabon, Brice Oligui Nguema, ya lashe zaben shugaban kasar, bisa ga sakamakon da aka fara fitarwa na wucin-gadi.
Sakamakon farko da aka sanar a ranar Lahadi ya nuna cewa Nguema, wanda ya jagoranci juyin mulkin soja a shekarar 2023, ya samu kusan kashi 80% na kuri’un da aka kada.
A bisa kashi 90.35% na kuri’un da aka kidaya, abokin hamayyarsa mafi kusa, Alain-Claude Bilie-By-Nze, ya samu kusan kashi 3% yayin da sauran ’yan takara shida ba su samu fiye da kashi 1% ba, in ji Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida ta kasar.
Nguema, wanda ya ba da gudunmuwa matuka wajen kawo karshen shekaru 55 na mulkin mallaka karkashin iyalan Bongo da tsohon shugaban kasa Ali Bongo ke jagoranta, an dade ana kyautata zaton zai lashe zaben ranar Asabar.