Kamfanonin kasar China da ke kera kayayyaki sun mayar da hankali kan Najeriya da sauran ƙasashen masu tasowa bayan kakaba harajin kan kayayyakin da shugaban kasar Amurka Donald Trump ya yi.
Trump, a ranar 2 ga Afrilu, Trump ya lafta harajin kashi 46% kan Vietnam da kuma harajin kashi 17% kan Philippines kafin ya mayar da shi kashi 10 cikin 100 na tsawon watanni uku masu zuwa, yayin da ya fara tattaunawar sulhu da kasashe kusan 75.
Masu masana’antu sun ce bayan da Amurka ta kara haraji kan kayayyakin China da kashi 145%, ya sa ‘yan kasuwar sun daina zuwa.