DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Ina burin na ga babu wani dan Nijeriya da ke shan wahala – Good Luck Jonathan

-

Tsohon shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi alkawarin ci gaba da sadaukar da rayuwarsa wajen inganta zaman lafiya da yi wa al’ummar Nijeriya hidima da ma duniya baki daya.

Jonathan ya bayyana haka ne a Abuja, yayin wani taron liyafa da abokansa suka shirya masa domin murnar karbar lambar yabo ta Sunhak Global Peace Prize Award ta shekarar 2025 a birnin Seoul na kasar Koriya ta Kudu.

Google search engine

Tsohon shugaban kasar ya ce a koda yaushe burinsa shine ya canza rayuwar al’umma wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali.

Jonathan ya ce duk da cewa ya sha wahala lokacin da yake yaro amma ya kan ji bakin ciki ya ga yadda ake shan wahala ko kuma ya ga wata kasa ta shiga mawuyacin hali.

Ya kara da cewa burinsa shi ne ya ga cewa babu wani dan Nijeriya da ke shan wahala, duk kuwa da cewa ba abu ne mai sauki ko mai yiyuwa ga wani shugaban kasa ya cimma hakan ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Limaman coci sun musanta zargin kisan Kiristoci a Nijeriya

Wasu limaman coci sun yi watsi da zargin Amurka da ke cewa ana gudanar da kisan kiyashi kan Kiristoci a Nijeriya.   Limaman sun mayar da martani...

Mun kashe Naira 100bn a fannin tsaron Borno cikin 2025 – Gwamna Zulum

Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya nuna damuwa da yadda ake kashe makuden kudade a fannin tsaro, yana mai cewa gwamnatinsa ta kashe Naira...

Mafi Shahara