DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Gwamnatin Tinubu ba ta da wani abu da za ta iya nunawa tun kafuwarta – Atiku Abubakar

-

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya soki gwamnatin Bola Tinubu kan manufofinta na tattalin arziki, yana mai cewa ba ta samu wata nasara ba tun kafuwarta.

A cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, Atiku ya ce gwamnatin Tinubu ba ta samu wasu nasarori da za ta iya tsayawa a kai, kuma ba ta da wani abu na tarihi da za ta iya nunawa, sai dai kawo hargitsi da rarrabuwar kawuna.

Google search engine

Furucin Atiku ya biyo bayan sauya sheka da wasu ‘yan jam’iyyar PDP suka yi a baya-bayan nan zuwa jam’iyyar APC.

A ranar Laraba ne gwamnan jihar Delta Sheriff Oborevwori da tsohon gwamnan jihar Ifeanyi Okowa suka fice daga jam’iyyar PDP zuwa jam’iyyar APC mai mulki.

Kazalika, dan majalisar wakilai Oluwole Oke ya fice daga jam’iyyar PDP ya koma APC a ranar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Majalisar dattawa ta bukaci a dauki matasa aikin tsaro domin magance matsalar tsaro

Majalisar dattawan Nijeriya, ta nuna damuwa kan tabarbarewar tsaro a ƙasar, tana kira ga shugaban ƙasa Bola Tinubu da ya amince da daukar matasa akalla...

Matukar dimokradiyya ta gaza a Nijeriya sai ya shafi fadin Yammacin Afrika – ECOWAS

Kungiyar tattalin arzikin kasashen Yammacin Afrika, ECOWAS, ta gargadi cewa duk wani rauni da dimokuradiyya ta samu a Nijeriya zai yi sanadin rushewar tsarin a...

Mafi Shahara