Mataimakin shugaban jam’iyyar Labour Party na kasa, Dr Ayo Olorunfemi, ya shawarci tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi da ya yi watsi da duk kiraye-kirayen ficewa daga jam’iyyar gabanin babban zaben 2027.
Olorunfemi, wanda shi ne dan takarar jam’iyyar LP a zaben gwamnan jihar Ondo a 2024, ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Nijeriya ranar Lahadi a Legas cewa ya kamata Obi ya mayar da hankali wajen sake gina jam’iyyar.
Olorunfemi, wanda ya bayyana cewa duk da cewa Obi na da ‘yanci shiga duk jam’iyyar da yake so, ya ce yana bukatar ya yi hattara sosai.