Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya ba da umurnin rufe duk wani asibitin da ba a yi wa rajista ba da kuma ma’aikatan jinya da ke aiki a babban birnin tarayya Abuja.
Babban mataimaki na musamman ga ministan kan harkokin yada labarai Olayinka ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Asabar.
Olayinka ya bayyana cewa ministan ya bayar da umarnin ne a lokacin da yake magana kan mutuwar wata mata mai juna biyu a wani asibiti mai zaman kansa da ke Durumi, Abuja, bayan tiyatar da aka yi mata.
A cewarsa, ministan ya yi gargadin cewa duk wanda aka samu yana gudanar da aikin ta haramtacciyar hanya ko kuma yana aiki a wani asibiti da bashi da rajista to a kama shi kuma a hukunta shi.



