DCL Hausa Radio
Kaitsaye

ECOWAS ta yi kira ga Nijar, Mali da Burkina Faso su sake shiga kungiyar

-

Majalisar kungiyar kasashen yammacin Africa wato ECOWAS ta yi kira ga kasashen Mali, Burkina Faso da Nijar da su sake nazari kan matakin ficewar cikin kungiyar.

A karshen wani taro na kwanaki biyar da majalisar ta yi a birnin Banjul na kasar Gambia, shugaban kwamitin hadin gwiwa Sanata Edwin Melvin Snowe Jr., ya jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin kasashen da ke yankin.

Google search engine

Sanata Edwin ya bayyana ficewar kasashen uku a matsayin wani abu da ya yi wa kasashen zafi, yana mai cewa kungiyar ta kasance a haɗe tsawon shekaru hamsin da suka gabata sai yanzu da kasashen suka fice.

Kasashe uku na yankin Sahel wadanda sojojin da suka yi juyin mulki ke jagoranta a yanzu, sun sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS ne a ranar 28 ga watan Junairu, 2024, kuma ficewar ta fara aiki ne a watan Janairun 2025.

Ukashatu Ibrahim Wakili
Ukashatu Ibrahim Wakilihttp://dclhausa.com
Ukashatu is a highly skilled and experienced broadcast journalist and fact-checker. Ukashatu has over five years of experience in writing, editing, and presenting news and program content for radio and television. As a dedicated and hardworking professional, He is committed to upholding the values of accuracy, fairness, balance, independence, and accountability in her reporting and programs.

1 COMMENT

  1. Baikamata sudawoba domin ECOWAS batada manifesto illa biyawa turawa bukatunsu,,
    Kuma kozasu komai sai bayan BOLA TINUBU yabar shugabanchin ECOWAS,
    Sanan a zauna a Yi sabon tsari domin samun chigaban Africa ta yamma da Kuma hadewar Africa guri daya,

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Dalori ya karbi ragamar jagorancin jam’iyyar APC a hukumance

Shugaban riko na jam’iyyar APC, Ali Bukar Dalori, ya bukaci shugabanni da mambobin jam’iyyar da su zauna cikin hadin kai bayan murabus din tsohon shugaban...

An dakatar da jirgin Rano Air kan zargin matsalar inji – NCAA

Hukumar kula da sufurin jiragen sama ta Najeriya (NCAA) ta dakatar da wani jirgin Rano Air mai lamba 5N-BZY bayan fuskantar hatsarin gobara da matsalar...

Mafi Shahara