DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Atiku ya caccaki Tinubu kan zargin cin zarafi da ake yi wa dansa Seyi Tinubu- Jaridar Punch

-

Madugun adawa a Najeriya, Atiku Abubakar, ya yi kakkausar suka ga shugaban ƙasa Bola Tinubu dangane da zargin azabtarwa da sace ɗalibi da ake yi wa ɗansa, Seyi Tinubu.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudana a Abuja, wani dalibi mai suna Atiku Isah, shugaban shiyya na Ƙungiyar daliban Najeriya (NANS), ya zargi Seyi da Ministan Ci gaban Matasa, Ayodele Olawande, da hannu a garkuwa da shi tare da azabtarwa tun a ranar 15 ga Afrilu bayan ya ƙi karɓar cin hancin Naira miliyan 100 da aka basu domin goyon bayan gwamnatin Tinubu.

Google search engine

Saidai a martanin da ya fitar a shafin Instagram, Seyi ya musanta haɗuwa da Isah ko shiga cikin irin wannan lamarin, inda ya bayyana zargin a matsayin ƙarya da aka ƙirƙira domin bata masa suna.

Atiku, ta bakin mai ba shi shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya yi Allah wadai da zargin tsoratar da shugaban ɗaliban, yana gargaɗin cewa Najeriya ba za ta zama mallakin iyalin shugaban ƙasa ba ko tsoratarwa daga gwamnati.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Fadar Shugaba Tinubu ta soki Atiku kan kwatanta gwamnatinsa da ta mulkin soja

Fadar Shugaban Nijeriya ta caccaki madugun adawa Atiku Abubakar, bisa kwatanta gwamnatin Tinubu da mulkin soja, tana mai bayyana kalaman nasa a matsayin abinda basu...

Majalisar Dattawa ta dakatar da muhawara kan gyaran dokar zabe tare da shiga zaman sirri

Majalisar Dattawan Nijeriya ta dakatar da muhawarar kan kudirin dokar zaɓe ta 2022, domin bai wa ’yan majalisa damar yin nazari mai zurfi kafin ɗaukar...

Mafi Shahara