DCL Hausa Radio
Kaitsaye

An ci tarar kudi ga wasu matasa bisa samunsu da laifin yunkurin safarar tururuwa a kasar Kenya

-

Wata kotu a ƙasar Kenya ta ci tarar wasu mutane hudu sama da dala $7,000 – daidai da kusan miliyan goma a naira – bayan an kama su da yunkurin fasakwaurin dubban tururruwa masu rai daga ƙasar ba bisa ka’ida ba.

Wadanda aka kama sun haɗa da David Lornoy da Seppe Lodewijckx – matasa ‘yan asalin ƙasar Belgium masu shekara 18 kowannensu, tare da Duh Hung Nguyen daga Vietnam, da kuma wani ɗan ƙasar Kenya mai suna Dennis Nganga.

Google search engine

Hukumar Kula da Dabbobi ta Kenya (KWS) ta zargi matasan da laifin ‘bio-piracy’ — wato satar halittu na ƙasa domin kasuwanci ko fasakwauri ba bisa ƙa’ida ba.

Rahotanni sun bayyana cewa an kama Lornoy da Lodewijckx dauke da kwalabe 2,244 da ke ɗauke da tururruwan sarauniya 5,000, a gundumar Nakuru da ke kusa da birnin Nairobi.

Duh da Nganga kuwa an same su da tururruwa a cikin 140 sirinjin allura da aka cike da auduga da kuma wasu akwati biyu.
Dukkaninsu sun amince da laifin mallakar tururruwan, sai dai sun musanta zargin fasa-kwaurin su zuwa ƙasashen waje.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Manyan Jami’an soji za su fuskanci ritayar dole bayan sauye-sauye a fannin tsaron Nijeriya

Rahotanni sun tabbatar da cewa akwai manyan jami'an sojin Nijeriya  masu mukamin Janar akalla 60 da za su fuskanci ritayar dole, biyo bayan sauye-sauyen da...

Rashin gogewar siyasa ta sa ban tsayar da El-Rufa’i don ya gaje ni ba – Obasanjo

Tsohon shugaban Nijeriya Olusegun Obasanjo ya bayyana cewa ya ki tsayar da tsohon gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Elrufa'i don ya gaje a shekarar 2007...

Mafi Shahara