DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Majalisar Dattawa ta amince da sabbin dokokin gyaran haraji -Akpabio

-

Majalisar Dattawa ta amince da dokoki biyu daga cikin muhimman dokokin gyaran haraji guda hudu da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya aike wa majalisar a watan Oktoba 2024.

Dokokin da aka amince da su sun hada da:

Google search engine
  • Dokar soke hukumar FIRS (Federal Inland Revenue Service),
  • da kuma dokar kafa sabuwar Hukumar Haraji ta Kasa da asusun hadaka na kudaden Haraji (Joint Revenue Board da Nigeria Revenue Service Bill 2025).

Majalisar ta amince da dokokin ne bayan nazari kai tsaye da karatu na uku a zauren majalisa.

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce wannan ci gaba zai inganta tafiyar da gwamnati da kuma saukaka tsarin tattarawa da raba haraji a kasar.

Ya kuma ce sauran dokokin biyu za a kammala su a ranar Alhamis, ko da hakan na bukatar tsawaita zaman majalisar.

 

 

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

Ćłan Nijeriya sun rage fita kasashen waje neman lafiya karkashin mulkin Tinubu – Rahoton jaridar Punch

Babban bankin Nijeriya, CBN ya bayyana cewa ’yan Nijeriya sun kashe dala miliyan 4.74 wajen neman lafiya a kasashen waje daga Mayu 2023 zuwa Maris...

Jam’iyyar PDP reshen Arewa maso Yamma ta nesanta kanta da Tanimu Turaki a matsayin dan takarar shugabancin jam’iyyar daga yankin

Jiga-jigan jam’iyyar PDP daga yankin Arewa maso Yamma sun nesanta kansu daga amincewar da aka yi da tsohon ministan ayyuka na musamman, Tanimu Turaki, SAN,...

Mafi Shahara