Jam’iyyar NNPP ta soki Engr Rabiu Kwankwaso bisa kiran wasu ‘yan Kwankwassiyya da suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC da sun yi butulci, jam’iyyar tana mai cewa Kwankwaso ne “babban butulu”.
A baya, Kwankwaso wanda tsohon gwamnan jihar Kano ne kuma jagoran tafiyar Kwankwasiyya, ya caccaki wasu manyan ‘ya’yan jam’iyyar NNPP a jihar Kano da suka sauya sheka zuwa APC kwanan nan, yana bayyana matakin nasu a matsayin zamba cikin aminci.
Jaridar Punch ta rawaito cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana haka ne a Kano, lokacin da wasu daga cikin jiga-jigan tafiyar Kwankwassiyya daga karamar hukumar Takai suka kai masa ziyara.
A cikin wata sanarwa da ya fitar a Lagos, shugaban jam’iyyar NNPP, na kasa Dr Agbo Major, ya ce Sanata Rabiu Kwankwaso ba zai iya magana da yawun jam’iyyar ba.
Sanarwar ta ce tuni an kori Sanata Rabiu Kwankwaso daga jam’iyyar NNPP tare da mabiyansa, karkashin jagorancin Dr Ahmed Ajuji.
A cewar Major, tafiyar Kwankwasiyya ba jam’iyya ba ce, illa wata kungiya ce cikin jam’iyyar NNPP a daidai lokacin zaben shugaban kasa na 2023, inda shugabanta ya zama dan takarar jam’iyyar.
Agbor Major ya bayyana cewa jam’iyyar NNPP ta ji abin mamaki, ganin yadda Kwankwaso ke kiran wasu daga cikin mambobin tafiyarsa da suka koma jam’iyyar APC da masu butulci.