Tsohon Gwamnan jihar Benue, Sanata Gabriel Suswam, ya yi gargadin cewa jam’iyyar PDP na iya rushewa kafin zaben 2027 idan shugabanninta ba su dauki matakan gyara matsalolinta ba cikin gaggawa.
Jam’iyyar PDP na cikin rikici kan wanda ya kamata ya rike mukamin sakataren jam’iyya na kasa.
Haka kuma, jam’iyyar ta fuskanci sauyin salo a ‘yan kwanakin nan, bayan da Gwamnan Jihar Delta, Sheriff Oborevwori, da wanda ya gada, Sanata Ifeanyi Okowa, tare da wasu tsofaffin shugabanni da mambobin jam’iyyar PDP suka sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.
Da yake magana a shirin The Morning Show na Arise TV, Suswam ya ce jam’iyyar PDP na cikin mawuyacin hali.
Ya bayyana cewa, da dama daga cikin mambobin jam’iyyar sun rasa kwarin gwiwa kuma suna jin ba za ta iya kai labari ba.