Wata babbar kotu a jihar Kano ta yi watsi da wata bukata da shugaban jam’iyyar APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje, ya shigar domin kalubalantar ikon kotun kan tuhumar cin hanci da ake masa da wasu mutane bakwai.
Mai shari’a Amina Adamu Aliyu, da ta jagoranci sauraron karar, ta bayyana cewa kalubalantar da Ganduje, tsohon gwamnan Kano, da sauran wadanda ake tuhuma suka gabatar ba su da tushe.
Gidan talabijin na Channels ya ba da labarin cewa Mai Shari’ar ta tabbatar da cewa kotun na da ikon sauraron karar da ta kunshi tuhume-tuhume 11, ciki ha da zargin karbar cin hanci, hada baki, karkatar da kuɗin jama’a da kuma batar da bilyoyin nairori.
Mai Shari’ar ta ce shari’ar za ta ci gaba duk da rashin halartar Ganduje da sauran wadanda ake tuhuma shida.
Haka kuma, ta ba da sammacin kan kamfanin Lamash Properties Limited, wanda shi ne na shida cikin wadanda ake tuhuma, tare da dage cigaba da sauraron karar zuwa ranar 30 da 31 ga watan Yuli.
Wadanda ake tuhuma sun hada da matar Ganduje, Farfesa Hafsat Umar, da wasu mutane da kamfanoni da suka hada da Abubakar Bawuro, Umar Abdullahi Umar, Jibrilla Muhammad, Safari Textiles Limited, Lasage General Enterprises Limited, da Lamash Properties Limited.