Majalisar wakilan Nijeriya ta ki amincewa da kudirin gyaran kundin tsarin mulki da ke neman a yi tsarin karba-karba a kujerar shugaban kasa da ta mataimakinsa tsakanin yankuna shida na kasar.
Haka kuma, majalisar ta ki amincewa da wasu kudirori shida na gyaran kundin tsarin mulki da aka saka a cikin jerin ajandar zaman majalisar a ranar Talata.
Sai dai, majalisar ta yanke shawarar dawo da wadannan kudirori a ranar Laraba domin ci gaba da nazarinsu daya bayan daya bisa cancantarsu ta musamman.



