Wata budurwa, dalibar sakandare mai kimanin shekaru 16, ta shirya karyar sace kanta tare da neman a biya kudin fansa har Naira milyan biyu don a sako ta.
Dalibar ‘yar ajin SS2 a wata makarantar sakandare mai zaman kanta da ke birnin Abakaliki na jihar Ebonyi ta tuntubi wani dan’uwa daga cikin iyalansu, inda ta yi ikirarin cewa an sace ta.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar, Joshua Ukandu, ya shaida wa manema labarai cewa wani makusancinta ne ya taimaka mata wajen shirya wannan karyar.
Sai dai ‘yan sandan ba su ambaci sunan dalibar ba da makarantar da take karatu.
‘Yan sandan dai sun ce har yanzu suna bincike kan wannan lamari domin tabbatar da hakikanin abin da ya faru.



