Tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya alakanta soke zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 12 ga watan Yunin 1993 da Marigayi MKO Abiola ya lashe da bashin Naira bilyan 45 na kwangila da Abiola yake bin gwamnatin mulkin soja ta Marigayi Janar Murtala Mohammed.
A cewar Lamido, an ki biyan Abiola bashin bayan rasuwar Janar Mohammed, kuma a lokacin da Abiola ya lashe zaben shugaban kasa, sai aka soke shi saboda fargabar cewa idan aka rantsar da shi a matsayin shugaban kasa, Abiola zai biyan kansa bashin, lamarin da ka iya durkusar da kasar a lokacin.
Sule Lamido ya bayyana hakan ne a ranar Talata a Abuja a lokacin kaddamar da littafin tarihin rayuwarsa mai suna ‘Being True to Myself’.