Jam’iyyar African Democratic Congress ADC ta sha alwashin hada akalla masu kada kuri’a miliyan 35 domin kawar da jam’iyyar mai mulki ta APC da kuma Shugaba Bola Ahmed Tinubu idan har ya nemi tazarce a shekarar 2027.
Shugaban jam’iyyar na kasa, Ralphs Okey Nwosu, ne ya bayyana hakan, yayin taron ADC Global Summit da jam’iyyar ta shirya a Abuja.
Nwosu ya yi tambaya kan sahihancin shugabanci da aka samu da kuri’u kasa da miliyan 10, yana mai tunatar da cewa an yi rajistar masu kada kuri’a sama da miliyan 88 a kasar kafin zaben 2023.
Ya ce jam’iyyar ADC na sake tsarinta da karfafa kanta domin fuskantar kalubalen zabe tare da farfado da kwarin guiwar masu kada kuri’a, wanda ya ragu matuka a zabukan baya.