By Salim Muhammad Musa
Kudurin na gyaran dokar zabe ta shekara ta 2022, ya tsallake karatu na biyu a majalisar wakilai a wannan Alhamis.
Idan har wani kudurin da ke gaban majalisa ya zama doka, za a tilasta wa kowane dan Nijeriya da shekarunsa suka kai na yin zabe, fita ya jefa kuri’arsa a rumfar zabe.
Kakakin Majalisar, Tajudeen Abbas, da kuma dan majalisa Daniel Ago ne suka dauki nauyin gabatar da wannan kudurin a zauren majalisa, a cewar jaridar Punch.
Daniel Ago ya bayyana cewa idan aka amince da wannan gyaran, zai magance dabi’ar nan ta kin yin zabe da wasu ‘yan kasa ke yi a lokacin da sauran yan uwansu ke can kan layi domin kada kuri’a.
Haka kuma ya ce dokar za ta ƙarfafa wa ‘ƴan ƙasa shiga tsarin zaɓe domin a dama da su wajen zaben shugabanni.
Duk da cewa ƙudirin ya tsallake karatun na biyu, dan majalisar wakilai na jam’iyyar PDP daga jihar Akwa Ibom, Mark Esset, ya ce yin doka kawai ba zai kawo chanji ga tsarin zaben kasar ba.
A cewar dan majalisar, mafi yawan ‘yan Nijeriya sun cire tsammani akan tsarin zaben kuma suna ganin cewa kuri’unsu ba sa da muhimmanci, shi ya sa ba sa fita su kada kuri’arsu a lokacin zabe.
Mark Esset ya ce idan har ana son wannan dokar ta yi aiki, to dole ne a tabbatar da cewa kuri’ar kowane dan kasa tana da tasiri a zabe.



