Akalla gidaje 300 ne suka rushe, tare da asarar dukiyoyi da darajarsu ta haura miliyoyin Naira, sakamakon wani hadari mai karfi tare iska da aka samu tare da ruwan sama a wasu unguwanni a birnin Katsina.
Lamarin da ya dauki kusan mintuna goma sha biyar da yamma bayan sallar La’asar a ranar Laraba, ya haddasa kwarewar rufin gine-gine kamar yadda gidan talabijin na Channels ya rawaito.
Daga cikin wuraren da lamarin ya fi shafa akwai Sabuwar Unguwar Modoji, Shinkafi, da yankin Kukar-Gesa, har da Ambassador Quarters da kuma wasu sassan karamar hukumar Jibia.
Mutane da dama, ciki har da wasu sabbin ma’aurata, sun rasa matsugunansu sakamakon wannan iftila’i.



