Kasar Afirka ta Kudu ta doke ‘yan wasan Flying Eagles na Nijeriya da ci 1-0 a wasan dab da na karshe na gasar cin kofin nahiyar Afrika na ‘yan kasa da shekaru 20.
An buga wasan ne a filin wasa na Suez Canal ranar Alhamis, don samun tikitin zuwa wasan karshe na gasar AFCON ta ‘yan kasa da shekaru 20 a kasar Masar.
Nasarar ta ba Afirka ta Kudu damar kaiwa wasan karshe na AFCON U-20 karo na biyu a tarihin ta, karon farko tun 1997, lokacin da suka kare a matsayin na biyu.
Ga Nijeriya kuwa, wannan shi ne karo na uku a jere da ta sha kaye a matakin wasan kusa da na karshe, bayan da Gambiya ta doke ta a shekarar 2023 da Mali a 2019.