Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu na wata ganawar sirri tare da shugabannin tsaro da Sufeto Janar na ‘yan sanda IGP a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
Cikin wadanda ke halartar taron akwai babban hafsan tsaro na kasa, Janar Christopher Musa; babban hafsan sojojin kasa, Janar Olufemi Oluyede; babban hafsan sojin sama, Air Marshal Hassan Abubakar; babban hafsan sojin ruwa, Vice Admiral Emmanuel Ogalla; da kuma sufeto janar na ‘yan Sanda, Kayode Egbetokun.
Duk da cewa cikakken bayani game da taron bai fito ba a lokacin hada wannan labarin kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito, amma ana hasashen tattaunawar na da nasaba da sake fasalin tsaro a sassan kasar.