Jami’an tsaro sun kama wani da ake nema ruwa a jallo bisa laifin garkuwa da mutane a sansanin aikin hajji da ke Abuja.
Wata majiya daga cikin jami’an tsaro da ke aiki a sansanin ta tabbatar wa da jaridar Daily Trust kama wanda ake zargin, a ranar Lahadi.
Majiyar ta ce an cafke wanda ake zargin ne yayin tantance mahajjatan da ke shirin tashi zuwa Saudiyya domin gudanar da aikin hajjin bana.
Majiyar ta bayyana cewa wanda ake zargin mai suna Yahaya Zango, mazaunin unguwar Paikon-Kore ne da ke karamar hukumar Gwagwalada a cikin babban birnin tarayya Abuja.
Jami’in tsaron ya ce hukumomin tsaro sun ayyana Yahaya a matsayin wanda ake nema, bisa zargin hannu da yake da shi a wasu laifukan garkuwa da mutane.
Ya kara da cewa wanda ake zargin ya gabatar da fasfonsa tare da sauran mahajjata daga Abuja da ke kan hanyarsu ta zuwa Saudiyya domin aikin hajji na bana.