DCL Hausa Radio
Kaitsaye

Hukumar tace finafinai ta jihar Kano ta dakatar da haska fim din Jamilu Jiddan da Garwashi da karin wasu 20

-

Hukumar tace fina-finai ta Jihar Kano ta dakatar da nuna wasu manyan fina-finai masu dogon zango har guda 22.

Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano karkashin jagorancin Alh Abba El-mustapha ta dauki wani gagarun mataki domin tsaftace yadda ake sakin fina-finai barkatai ba tare da cika ka’idar da doka ta tanadar musu ba na kawo kowane film gabanta a tantance shi kafin ya isa ga idanun al’umma, inda ta dakatar da wasu Manyan Fina-finai har guda 22 daga saka su a kafafen Internet ko gidan TV.

Google search engine

Abba El-mustapha ne ya bayyana wannan mataki biyo bayan tattaunawa da manyan jami’an Hukumar tare da dogon nazari domin kawo karshen korafe-korafen da Hukumar take yawan karba dan kara inganta aiyukan Hukumar tare da masana’antar kannywood.

Abdullahi Sani Sulaiman jami’in yada labaran Hukumar, a cikin wata sanarwa da DCL Hausa ta samu kwafi, ya bayyana fina-finai da aka dakatar kamar haka:

1. Dakin Amarya
2. Mashahuri
3. Gidan Sarauta
4. Wasiyya
5. Tawakkaltu
6. Mijina
7. Wani Zamani
8. Labarina
9. Mallaka
10. Kudin Ruwa
11. Boka Ko Malam
12. Wa yasan Gobe
13. Rana Dubu
14. Manyan Mata
15. Fatake
16. Gwarwashi
17. Jamilun Jiddan
18. Shahadar Nabila
19. Dadin Kowa
20. Tabarma
21. Kishiyata
22. Rigar Aro

Ya kara da cewa doka ce ta bawa Hukumar damar tace duk wani film tare da lura da aiyukan ‘yan masana’antar kannywood matsawar suna da rejista da Hukumar a ko ina suke, A saboda haka ana shawartar masu daukar nauyin wannan fina-finai da su tabbatar da sunbi wannan doka ta dakatarwa tare da tsayar da saka wannan fina-finai a gidajen TV ko kafar internet. Haka kuma ana sanardasu cewa su miko fina-finansu ga Hukumar domin tantance su tare da basu shaidar inganci ta tacewa nanda sati daya mai zuwa wato daga *LITININ, 18 ga watan MAYU, 2025 zuwa 25 ga MAYU, 2025* domin gujewa fushin doka.

A karshe Hukumar ta nemi hadinkan dukkannin gidajen TV da Hukumar dake lura da kafafen yada labarai ta Nijeriya wato NBC kan su cigaba da taimakawa Hukumarsa domin samun nasarar abinda ta saka a gaba da cigaban Jihar Kano da masana’antar kannywood.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Sabbin Labarai

’Yan majalisar wakilai bakwai daga Akwa Ibom sun sauya sheka zuwa APC

Ana cigaba da samun rahotannin sauyin sheka a majalisar wakilai, yayin da ’yan majalisa bakwai daga Jihar Akwa Ibom suka koma jam’iyyar APC. Wadanda suka...

Jam’iyyar Labour tsagin Julius Abure ta ba Peter Obi sa’o’i 48 ya fice daga jam’iyyar saboda shiga hadakar ADC

Jam’iyyar Labour karkashin jagorancin Julius Abure ta bai wa tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi, wa’adin sa’o’i 48 da ya fice daga jam’iyyar, bisa...

Mafi Shahara