Tsohon shugaban kasar Amurka, Joe Biden, na fama da cutar daji wato ‘cancer’ wadda ta bazu zuwa cikin kasusuwansa, kamar yadda ofishinsa ya sanar.
Joe Biden, mai shekaru 82, an gano yana da cutar ne bayan likitoci sun gano wani kumburi a sassan jikinsa.
An kai tsohon shugaban asibiti domin a duba shi bayan ya fara fama da yawaitar fitsari.