Kungiyar Kwankwasiyya Coalition of Concern Citizens mai fafutuksr tabbatar da cigaba, ta gargadi Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano da, ya kula da ‘yan bani na iya a gwamnatinsa da ake kira “Cabals”
Wannan jan hankali na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban kungiyar na kasa, Kwamared Dayyib Hassan Ahmad ya rabawa manema labarai.
A cewar sanarwar, hanyar da wasu ‘yan majalisar zartaswa suke gudanar da ayyukansu bai dace da kokarin gwamnan na ganin Kano da al’ummarta sun samu ci gaba ba.
Ya bayyana cewa kungiyar da aka kafa tun shekarar 2019 ta ga ya dace a ja hankalin gwamnan da ya yi taka-tsan-tsan da wasu daga cikin abokan aikinsa domin ba sa yin abinda ya kamata.
Sanarwar ta ce abin damuwa ne a ce an bar mutanen da suka yi kokari wajen ganin an samu nasarar jam’iyyar NNPP a Kano ba a kula da su ba, ya yi zarigin cewa wasu jiga-jigan gwamnatin ba su yi wani abin da ya taimaka wa gwamnatin Gwamna Abba ba, duk sun fito ne don neman biyan bukatun su ba wai yi wa al’umma aiki ba.