Hukumomin Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin daya cikinsu ita ce mahaifiyar Ado Aliero, fitaccen shugaban ‘yan bindiga a Najeriya.
Majiyoyi sun ce jami’an leken asiri ne suka kama su a Madina, bisa zargin suna da alaka da masu ta’addanci daga Arewa maso Yammacin Najeriya.
Ado Aliero na daga cikin manyan ‘yan bindiga da ake nema ruwa a jallo kan laifukan garkuwa da mutane da hare-hare a Zamfara da makwabtanta.