Tsohon gwamnan jihar Jigawa kuma tsohon sakataren jam’iyyar SDP, Sule Lamido, ya bayyana cewa shi da marigayi Abubakar Rimi sun ƙi karɓar cakin kuɗi na Naira miliyan 160 da marigayi Abba Kyari ya kawo musu domin samun goyon bayansu a matsayin mataimakin Olusegun Obasanjo a shekarar 1999.
Lamido ya bayyana hakan ne a cikin littafin tarihin rayuwarsa mai suna “Being True to Myself”, inda ya ce Kyari ya kawo takardar banki ne da sunan taimaka wa jam’iyyar PDP wajen kamfe, amma suka ƙi amincewa kuma inda ya tashi cikin kunyata.