Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya mayar da martani ga masu cewa gwamnatinsa na kokarin kafa tsarin jam’iyya daya a Najeriya, inda ya ce ba za a zargi mutane ba idan sun zabi inda za su shiga.
Da yake jawabi a taron kolin APC a fadar shugaban kasa, ya ce: “Jam’iyya daya ce ke mulki yanzu. Idan jirgin da kake ciki na nitsewa, ba za a zarge ka ba idan ka nemi hanyar tsira.”
Ya kara da cewa APC a shirye take ta karbi ‘yan Najeriya da ke son shiga jam’iyyar, yana mai cewa; Ba za a tilasta wa kowa zama inda bai so ba. Mu ‘yan gaba-gaba ne, za mu ci gaba da jajircewa wajen kunyata masu neman gazarmu.



